Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morocco Zata Iya Shiga Wasannin CAF Daga Yanzu


CAF
CAF

Hukumar kwallon ‘kafar Afirka (CAF) a takaice, ta tabbatar da cewa kasar Morocco zata iya shiga wasannin share fage na cin kofin nahiyar Afirka da za’a yi a shekara ta 2017.

CAF ta dakatar da kasar Morocco daga shiga wasannin ta na shekara ta 2017 dana shekara ta 2019, da tarar dala miliyan ‘daya, a dalilin janye kanta da tayi na karbar bakuncin wasan cin kofin Afirka da akayi na shekarar data wuce.

Morocco dai ta janye daga karbar bakuncin wasan a dalilin tsoron yaduwar cutar Ebola, alokacin da cutar ta addabi yammacin Afirka a dai dai lokacin da aka shirya yin wasan na watan Janairu da Fabarairu.

Kotun sauraren kararrakin wasannin motsa jiki ce ta canza hukuncin da hukumar wasan ta yanke a ranar Alhamis ‘din data wuce, biyo bayan ‘daukaka karan da Kasar Morocco tayi.

A shafin yanar gizo na hukumar kwallon kafar sun kafe cewa, CAF ta kuduri aniyar amfani da hukuncin da kotun CAS ta yanke, duk kuwa da dalilan da kotun tayi amfani dasu wajen yanke hukuncin.

XS
SM
MD
LG