Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mujallar Duniyar Computer Na Taimakawa Hausawa Kan Ilimin Fasaha


Duniyar Computer wata mujalla ce dake kan yanar gizo da take fitowa kowane satin farko a wata, tana kuma taimakawa mutane wajen warware dukkannin matsaloli da suke fuskanta ta fannin na’ura mai kwakwalwa.

Salisu Hassan wani matashi ne da yayi amfani da ilimin sa wajen kirkirar wannan mujallar dake kan yanar gizo da ake kira Duniyar Computer. Kasancewar yanayin canjin da na’ura mai kwakwalwa ta kawo a cikin al’umar Hausawa, yana da matukar yawa da amfani.

Kafin ya bude Duniyar Computer, a tabakin Salisu Hassan yace mutane na ganin ba yadda za’ayi su iya sarrafata, haka kuma wasu dayawa sun jahilci ilimin Kwamfuta ne a baya, inda wasu malamai ke cewa amfani da ita ma bai halarta ba, Salisu ya kuma duba yaga cewa ya za’ayi ace abin da zamani yazo dashi ace bai halarta ba, ya kuma tuntubi manyan malamai wanda suke da sanin zamani da kuma addini, sun dai shaida masa cewa wannan abune da kowa yakamata ace ya iya yinsa.

Hakan ne yasa Salisu ya tashi tsaye wajen wayarwa mutane kai kan ilimin na’ura mai kwakwalwa, wanda hakan ke taimakawa mutane da dama wajen wayewa da samun sauki a rayuwa, idan aka duba yadda komai ya koma kan yanar gizo a wannan zamani.

XS
SM
MD
LG