Najeriya, mai babbar kungiyar kwallon kafa Super Eagles, ta bayana aniyar dakatar da zuwa gasar cin kofin duniya, domin kowanne lokaci maimakon samun haske sai duhu ake gani, inda akwai lokacin da Najeriya, bata samun gurbin zuwa gasar daga matakin Afirka.
Najeriya, dai ta fara samun damar zuwa gasar na cin kofin duniya ne tun shekarar 1994, a lokacin da akayi gasar a kasar Amurka, inda Rasheed Yekini, ya shiga tarihi a matsayin wanda ya fara ciwa Najeriya kwallo a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Gasar na cin kofin kwallon kafa na duniya an dai fara shine a karon farko a shekarar 1930.
Yadda lamura ke gudana in ji Ministan matasa da wasani Barrister Solomon Dalung, na nuna cewa Najeriya, bata kama hanyar lashe gasar ba har abada domin haka ci gaba da zuwa gasar tamkar yankawa kare ciyawa ne.
Ministan ya ce “ Kofin da za’a dauka shine na Africa, tunda yake ana da wasani kamar na Common wealth kasashe renon Ingila, na Olympic da take hada duniya za’a iya haduwa a irin wannan amma maganar kwallon kafa ta duniya wanda za’a ce aje a taru a can bamu yard aba munafincita na da yawa ga maganar bada cin hanci da rashawa kafin kasar ku ta samu izinin daukar nauyin wasan”.