Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na'urori Sama Da Miliyan 300 Ne Ke Amfani Da Window 10 A Duniya


Kamfanin Microsoft, ya bayyana cewa yanzu haka akwai na'urori Miliyan 300 dake amfani da sabuwar manhajar window 10 a fadin duniya. Da wannan ci gaban, Window 10 ya shiga cikin jerin kayayyakin fasaha da suka samu karbuwa a kasa da shekara guda.

Microsoft yace yana tsammanin ganin yawan mutanen dake amfani da Window 10 ya karu, kuma kamfanin na son ganin duk masu na’urorin kwamfuta dake da manhajar Window 7 sunyi amfani da damar da suke da ita wajen sabunta manhajarsu ba tare da biya ko sisin kwabo ba, kafin karshen watan Yuli.

Akwai app masu yawan gaske kunshe cikin manhajar Window 10, haka kuma an tsara manhajar domin saukakawa masu amfani da ita wajen aiwatar da dukkan aikinsu cikin sauki, da samun duk abinda suke nemi.

Ita dai wannan manhaja mutane kan iya samunta kyauta har zuwa 29 ga watan Yuli, bayan wannan rana kuwa duk wanda ke bukata zai iya sayenta a $119.

XS
SM
MD
LG