Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neman Aure A Da Ya Banbanta Da Na Yanzu


Kamar yadda wasu matasa 'yan mata da samari suka bayyana nasu ra'ayoyin musammana akan irin dalilan da zas su sa hankalin su ya karkata wajan amincewa da auren abokan soyayyar su, mun zanta da wasu iyaye maza da mata inda suka bada nasu ra'ayoyin kamar haka;

Da farko dai lokacin da duniya na kwance yawanci akan daura ma yarinya aure da saurayin da ta kawo gidan su, kuma hakan bashi da wata miskila saboda komi akan gaskiya ake yin sa. kamar yadda wata mata ta bayyana, ranar da saurayin na ta ya zo gidan su ranar ya fada mata da aure yazo nemanta.

Shin ana yin irin haka a wannan zamanin kuwa?

Haka wani magindaci ya bayyana ra'ayinsa sai dai shi ya kara da cewar lallai abin da aka fi la'akari da shi a lokacin su shine tarbiyar gida, ya kara da cewar a yanzu yawancin samari da 'yan mata kan hadu ne akan titi kuma abin mamaki har su yarda su auri juna daga karshe.

Daga karshe sun yi kiraye kiraye musamman ga iyaye cewar ya kamata iyaye su kara sa ido akan wayar hannu da yaran su ke anfani da ita domin kuwa a cewar su tana kara lalata tarbiyar matasa.

Saurari karin bayani.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG