Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Neman Hakki Wurin Gwamnati


Jonah Jang
Jonah Jang

‘Yan Fensho a jihar Filato, sun gudanar da wani zanga-zangar lumana na neman Gwamnati da ta biyasu hakkokinsu.

Shugaban kungiyar ‘yan fenshon na kasa rashen jihar Filato, Danladi Jimoh, yace dayawan ‘yan fenshon sun mutu saboda rashin abun biyan bukata, kuma akazarinsu sun kamu da cutar sikari.

Ya kara da cewa yawancin ‘yan kungiyar na fama da rashin lafiya, inda kuma akazarinsu suka kamu da cutar sikari, kuma sun yi koke-koke ga Gwamnati, har yanzu shuru.

Ya cigaba da rokon Gwamnati, da ta dubaisu da idon rahama ta biya masu bukatunsu ko suma zasu samu saukin kuncin rayuwa.

Yana kuma mai cewa zanga-zangarsu bata da wani nasaba da siyasa, su dai hakkinsu suke nema a wurin Gwamnati, abunda yake halaliyarsu suke kuka aka.

Shugaban ma’aikatan jihar Filato, Eziekel Daliyop, yayi alkawarin cewa nan bada jimawaba Gwamnati, zata biya su hakokinsu.

'Yan Fensho - 3'54"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

XS
SM
MD
LG