WASHINGTON, DC —
Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa, yace gazawar hukumomin Najeriya ne ba wai ta makwabtanta ba, har ‘yan Boko Haram suke yin abubuwan da suke yi. Gwamnan yana magana ne yayin da hukumomin Najeriya ke zargin makwabtanta da bayarda mafaka ga ‘yan Boko haram din, ko kuma ba su daukar matakan hana su yin amfani da yankunansu wajen kai hari kan Najeriya.
Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara, shi ma yace da walakin ganin yadda Boko Haram ke cin karenta babu babbaka a yankin arewa maso gabashin kasar. Gwamnan na Zamfara yace ko dai akwai sakaci, ko kuma irin daurin gindin da kungiyar ke samu ya shiga wasu manyan sassan da ba a bayyana ba. Gwamnonin arewacin Najeriya su na shirin ganawa domin tattauna wannan batu na tsaro, a bayan wani taron da suka yi makon jiya a nan Washington.
Jam’iyyar PDP ta koka da ganin cewa ya zuwa yanzu kujeru 4 rak ta samu a zaben kananan hukumomi na Jihar Nassarawa. Wani babban jami'in PDP na kasa yace ana nema ne a haddasa tashin hankali ta hanyar yi musu kwace a jihar ta Nassarawa. Jam’iyyar APC dai ta yi watsi da wannan korafin na PDP a zaman maras tushe, ta kuma ce duk mai wata kuka yana iya gabatarwa a gaban hukumomin da suka dace.