Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Gata na Komar da Al'umma Baya


Hauka
Hauka

Rashin galihu babu abun da bai haifarwa a rayuwar dan’adam, dadamar al’uma kansamu kansu cikin wasu halaye wadanda bai kamata ace suna ciki ba, amma saboda wasu dalilai da basu taka kara sun karya ba sai ka same su cikin halin ha’ulai. A irin wanna dalilin ne wata baiwar Allah me suna Malama Nabawiyya Dahiru, ta ke mika kukanta ga al’uma masu hannu da shuni dama masu karamin karfi, dasu yi amfani da dukiyar su wajen ceto irin wadannan mutane daga wani irin mumunan hali na rayuwa.

Ta kasance takan ziyarci gidan masu tabin hankali dake Dorayyi a jihar Kano, a kowace ranar Juma’a don taimakama mutanne da ke fama da tabin hankali, sukan kai abun da befi karfinsu ba wajen taimaka musu.

Babban abunda suke yi su kan girka musu abinci me gina jiki, da kuma taimaka musu da wasu shawarwari da dai duk abu daya kama, ganin cewar wasu daga cikin su sun samu kansune cikin halin kuncin rayuwa wanda yayi sanadiyyar zamansu masu tabin hankali, wanda idan aka duba za’aga cewar suna bukatar abubuwa kadanne don samun sauki daga halin da suke ciki, amma saboda hali da suka samu kansu ciki na rashin gata da me bada shawara sai ka ga sun kare a irin wannan gidajen.

Don haka don Allah al’uma suyi amfani da dukiyar da Allah ya basu wajen amfani da ita don taimaka ma gajiyayu, don wannna shine koyarwar kowane irin addini, don ta haka ne kawai mafi akasarin wadannan mutane zasu samu kansu cikin jin dadi da walwala kamar sauran mutane, da Allah ya halitta don ibada.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG