Batun rashin jituwa da ake samu tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma na daga cikin abubuwan dake kara kalubalen tsaron a wasu sassan Najeriya.
Jihohi irin su Taraba, Filato da Kaduna da Zamfara, na daga cikin wadanda suka yi kaurin suna wajen rikicin makiyaya da Manoma, lamari dake gai ga hasarar dukiyoyi dama rayukan bil-Adama, a wasu lokuta.
Rikici dai tsakanin wadannan bagarori guda biyu na alumar Najeriya, na tada hankulan jama’ar kasar masamma ma mahukunta, ta la’akari da rawar da suke takawa ga bunkasar tattalin arzikin kasa.
Akan haka ne yasa Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi, na biyu ya jaddada kiran zaman lafiya ga makiyaya, lokacin da shuwagabanin kungiyar Miyetti Allah na kasa suka ziyarci fadar sa.
Shi kuwa Gwamna Jigawa Sule Lamido, cewa yake daukar matakan kula da hakkokin Makiyaya da dabbobinsu sune zasu kawo karshen zaman tankiya tsakaninsu da Manoma, domin kuwa in ji shi sun gwada sun gani a jihar Jigawa.