A yau za'a dawo filin daga a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai Uefa Champions league, na shekarar 2016/17 a matakin wasan kusa da na karshe (Quarter final).
Wasan zai kasancene tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, da takwararta ta Atletico Madrid, dukkan su 'yan Kasar Spain.
A tarihin wasa tsakanin kungiyoyin biyu an hadu sau arba'in da ukku Inda Real Madrid, ta yi nasara a kan Atletico Madrid, sau 25 ita kuma Atletico Madrid, sau 7 kacal ta taba samun nasara a kan Real Madrid, anyi kunnen doki sau 11.
A karawarsu ta karshe an tashi 1-1 a gasar laliga na bana wanda akayi ranar 8/4/2017 a gidan Real.
Manyan ‘yan wasan kwallon kafa irin su Cristiano Ronaldo, na Real Madrid, da Antoine Greizmann, na Atletico Madrid, za su haskaka a wasan, kuma za'a buga wasanne da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar da kamaru a filin wasa na Santiago Bernabeu, mai daukan mutane 85454.