Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Ce Ta Kashe 'Yan Ta'adda 40 A Bulanbuli Kusa Da Dajin Sambisa - 25/4/2014


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya
Rundunar sojan Najeriya ta fada yau jumma'a cewa ta kashe 'yan ta'adda su fiye da 40 a wani fadan da aka gwabza a Bulanbuli, kusa da dajin nan na Sambisa. Rundunar ta ce an kashe sojoji 4 a wannan fada da mayakan da aka ce 'yan Boko Haram ne.

Kakakin hedkwatar rundunar tsaron Najeriya, Manjo-janar Chris Olukolade, yace fadan ya barke a bayan da aka kama wasu mutanen da ake tsammanin manya ne a kungiyar Boko Haram a kewayen yankin Alagarno.

Kakakin yace kwanaki biyu da suka shige aka kama 'yan ta'adda guda biyu su na sayen kayan abinci a wata kasuwa, yayin da wasu suke leken asirin wani sansanin soja dake kusa da nan. Yace har yanzu ana bin sawun wani da ake jin cewa ma'aikacin kiwon lafiya na 'yan ta'adda ne dake kokarin saya musu magunguna.
XS
SM
MD
LG