Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin Gwamna Adamawa, Bala James Ngillari, da kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara Ahmed Ali Gulak, game da takarar kujerar Sanata, na mazabar Adamawa ta arewa, inda kowane ke ikirarin cewar shine dan takarar Sanata, na jam’iyyar, PDP, a mazabar.
Tun farko dai Ahmed Ali Gulak, shine aka bayyana cewa ya lashe zaben fidda gwani na kujerar sanata, a mazabar Adamawa ta arewa, yayi da Gwamnan ke cikin mutane shida da suka yi takarar Gwamna na jam’iyyar PDP, amma kuma jam’iyyar ta bayyana sunan Nuhu Ribadu, cewa shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar Gwamna.
Amma kuma kwanaki biyu baya sai kuma aka bayyana suna Gwamna Bala James Ngillari, cewa shine dan takarar Sanata, a mazabar, Adamawa ta arewa, batun da ya sake jawo ce-ce- ku-ce a faggen siyasar jihar.
Sai dai wannan mataki na sauya dan takara da jam’iyyar ta dauka bai yiwa Ali Gulak dadi ba domin a wani taron manema labarai da ya kira a Yola fadar jihar Adamawa, yace Gwamna Ngillari, takarar Gwamna ya tsaya bai tsaya na Sanata ba, kuma bai cika takardan neman Sanata ba.
A nasa martanin Gwamna Ngillari, ta bakin kakakinsa Mr. Elisha, yayi watsi da korafin da Gulak, keyi, yana mai cewa sunan Ngillari, ke INEC, a matsayin dan takarar Sanata na Adamawa ta arewa.