Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin La-Liga Da Firimiya Lig Na Ingila


A wasannin da aka fafata a La-Liga na mako na ashirin da takwas a can Kasar Spain a ranar jumma'a da ta gabata Kungiyar kwallon kafa ta las Palmas ta doke Villarreal 1-0, ranar asabar kuwa Eibar tayi kunnen doki 1-1,da Espanyol, Athletic Bilbao tasha kashi a hannun Real Madrid da kwallo 2-1, Alaves ta samu nasara akan Real Sociedad daci 1-0, Real Betis ta doke Osasuna 2-0.

A jiya lahadi Leganes tayi canjaras da Malaga 0-0, Atletico Madrid ta lallasa Sevilla kwallaye 3-1, Deportivo ta sha kashi a hannun Celta Vigo, 1-0, Sporting Gijon ta doke Granada da ci 3-1,Barcelona ta lallasa Valencia da kwalaye 4-2.

Kungiyar Real Madrid ke Jan ragamar teburin da maki 65, Barcelona a mataki na biyu da maki 63, Sevilla tana mataki na uku da maki 57, Sporting tana mataki na sha takwas a kasan teburin da maki 21, Granada tana mataki na sha tara da maki 19, sai Osasuna da take mataki na ashirin da maki 11.

A bangaren Firimiya lig na Kasar Ingila kuwa an buga mako na ashirin da tara ne inda West Bromwich ta lallasa Arsenal da ci 3-1,Stoke City tasha kashi a hannun Chelsea da kwallaye 2-1, Westham Nada 2 Leicester city Nada 3, Everton ta lallasa Hull City da kwallaye 4-0, Crystal palace 1-0 Watford, Sunderland da Burnley sun tashi babu ci, AFC Bournemouth ta doke Swansea 2-0.

A jiya lahadi kuwa, Middlesbroug tasha kashi a hannun Manchester United da kwallaye 3-1,Manchester City tayi kunnen doki 1-1 da Liverpool, Tottenham 2 Southampton 1.

Chelsea tana mataki na daya a saman teburi da maki 69, Tottenham ta na biye da maki 59 sai Manchester City a mataki na uku da maki 57.

A kasan teburin kuwa kungiyar kwallon kafa ta Hull City ke mataki na sha takwas da maki 24 sai Middleborough a mataki na sha tara da maki 22, Sunderland tana kasan tebur a matsayi na ashirin da maki 20.

XS
SM
MD
LG