Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasanin La-Liga Da Firimiya Lig


A wasannin da aka fafata a kasar Spain bangaren La-Liga na shekara 2016/2017 mako na talatin da biyu ranar Jumma'a da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao ta lallasa Las Palmas da kwallaye 5-1.

Ranar Asabar 15/4/2017, Deportivo ta doke Malaga da ci 2-0 Sporting Gijon tasha kashi a hannun Real Madrid da kwallo 3-2, Atletico Madrid ta samu nasara akan Osasuna da kwallaye 3-0, Barcelona ta doke Real Sociedad da kwallo 3-2.

A jiya lahadi kungiyar kwallon kafa ta Real Betis ta doke takwararta ta Eibar da ci 2-0,

Leganes 0 Espanyol 1. Valencia tayi kunnen doki 0-0 tsakaninta da Sevilla, Granada tasha kashi a hannun Celta Vigo da kwallaye 3-0.

A yau kuma za'a kara tsakanin Alaves da Villarreal da misalin karfe takwas saura kwata agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ke Jan ragamar teburin da maki 75, Barcelona tana mataki na biyu da maki 72 sai Atletico Madrid a mataki na uku da maki 65.

A kasan teburin kuwa Sporting Gijon tana mataki na sha takwas da maki 22, Granada tana mataki na sha tara da maki, 20 Osasuna na mataki na ashirin da maki 17.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

XS
SM
MD
LG