Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samartaka A Watan Ramadana


Watan Ramadana wata ne na ibada da yakamata dukkan musulmi ya zauna cikin tsarki da kuma aikata ayyukan alkhairi domin samun lada daga mahaliccinsa, kuma malamai a kowane lokaci na ci gaba da yin bakin kokarin su wajan fadarkarwa da tunatar da jama'a manya da yara a kan falalar wannan wata.

Ta dalilin haka ne muka nemi jin ta bakin matasa maza da mata musamman akan yadda suke tafiyar da al'amurran su na yau da kullum domin abubuwa da dam kamar zuwa zance, kiran juna ta waya har ma ganawa da juna a wasu lokuta a wannan lokaci.

Da farko mun ji ra'ayin wani saurayi wanda ya nuna cewar lallai yana kiyaye wa a kowane lokaci musamman ganin yadda ya taso a gidan su, kuma yaga yadda sauran nagaba da shi ke gudanar da sha'anin rayuwar su.

Koda shike mun sami labarin cewa akwai samari da 'yan mata da dama dakan yi karyar zuwa tafsir ko masallaci musamman 'yan matan da iyayen su ke hana su fita, kan yi amfani da wannan dama domin ganawa da samarin su.

Masu iya magana dai sun ce bin nagaba bin Allah, dan haka matasa a yi hattara, domin bai kamata a kauce hanyar ibada ba domin samun makoma mai kyau.

Aikawa juna sakonnin hotuna ko bidiyon da basu dace ba ka iya bata maka azumi, kuma a tuna akwai hisabi akan duk abin da mutum ya aikata. matasa a yi hattara.

Ga cikakkiyar hirar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:16:51 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG