WASHINGTON, DC —
Sana’ar Awara yafi zaman kashe wando inji Malama Fatima Abubakar, takuma kara da cewa sana’arta shine gatanta alokacin da take zantawa da wakiliyar Dandali VOA.
Malama Fatima dai tace ita sana’ar ta itace yin Awara da sayar da ita ga mata da yara, tace ana yawan zuwa ana sayan Awarar ta saboda akwai wasu sinadarai masu kara lafiya ga jikin mutane, tana kuma yin Awarar takuma sarar da ita ga wasu masu irin sana’ar tata. Kuma tana sayar da kala, ana dai amfani da kala wajen hada abubuwan sha kamar Zoborodo da dai sauransu.
Fatima dai ta rike wannan sana’ar tata da muhimmanci kuma bisa ga dukkan alamu tana samun yiwa kanta duk wasu abubuwan rayuwa da take bukata a rayuwarta. Saurari cikakkiyar hirar Baraka Bashir da Malama Fatima.