A shirinmu na cigaban matasa, koma ince matasa masu neman cigaba ta hanyar zamantakewa, ilmi dama siyasa, a yau zakuji hirar wakiliyar Dandalin VOA da wani matashi mai sana’ar dukanci, wanda da wannan sana’ace ya kammala karatunsa na sakandare har ma da zuwa jami’a.
Wannan matashi mai suna Alkasim Adamu Darma dai ya bayyana mana yadda ya fara wannan sana’a dama kalubalen daya fuskanta, inda yace, “sana’a ta dukanci, abinda yaja hankalina zuwa sana’ar dukanci shine naga abokaina na sana’ar dukanci to sakamakon ina ‘dalibci a makarantar sakandare kuma bani da sana’a alokacin sai dai abinda aka bamu a gida, shine nayi kokarin na fara sana’a irin ta abokanena nafara zuwa gurunsu ina kallon yadda suke gabatar da wannan sana’ar tasu har na samu wani jari a hannun wani abokina, ya rantamin jari da bai taka kara ya karya ba a shekaru na naira dubu daya da shina fara sana’a ta.”
Mallam Alkasim Adamu Darma, yadai cigaba da bayyana godiyar sa kan samun nasarori dayayi dalilin wannan sana’a, yadai karasa karatunsa na gaba da firamare da ita, harma ya koyawa wasu yara yin sana’ar dukanci harda ma mata ya koyawa sana’ar. Saurari tabakin Alkasim Adamu Darma a hirar da sukayi da wakilarmu Baraka Bashir.