Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SANARWA: VOA Flamingo FC Ta Fita Daga Kungiyar GRAFCA Bauchi


Amadadin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Voa Flamingo Fc da ke garin Bauchi

Suna sanar da ‘yan wasansu da kuma magoya bayan kungiyar da dukkan masu sha'awar kwallon kafa a jihar Bauchi cewar daga ranar Talata 5/4/2017 kungiyar ta VOA flamingo, ta fita daga cikin kungiya mai suna GRAFCA Bauchi, saboda wasu dalilai wadanda nan gaba shuwagabanin kungiyar ta Flamingo zasu baiyana.

Kuma shuwagabanin kungiyar suna kara sanarwa da ‘yan wasa da magoya baya cewar kungiyar ta VOA flamingo, daga yau ta koma karkashin jagoranci kungiya masu son ciyar da harkar kwallon kafa gaba wato Bauchi progressive football Association, wannan matsaya da aka dauka ya biyo bayan zaman da shuwagabaninta sukayi a yau 5 ga watan Afirillu alif dubu biyu da goma sha bakwai don haka flamingo is One family.

Sanarwa daga Bala Branco.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG