Mus’ab Dauda wanda aka fi sani da Hausa Top – Wani shafin Internet da ake yada wakoki da labarai da suka shafi nishadi, musamman ma na mawaka, Mus’ab ya zabi hanyar ce, domin saukakawa mawaka wajen tallata hajjarsu ga duban al'umma a sassan duniya daban-daban.
Bayan shafin sadarwar na Internet da suke zuba labaran mawaka, sun kuma fito da talabijin, amma na Internet wanda ya fara aiki, yana mai cewa wannan al’amari ne na shekaru uku nan gaba.
Babban dalilin abinda ya sa ya fara wannan shafi, shine a kudancin Najeriya, tuni suka yi nisa da irin wannan cigaba, wanda yake bawa mutane a kowanne sassan duniya samun bayanai da suka shafi mawaka da sabbin wakokinsu a saukake.
Sabon mawakin da ya ke so a saka labarinsa akwai wani gurbi na tuntuba da mawaki zai iya tura bayanai da yake bukata, sannan ana biyan wasu kudaden kafin a sanya wakar mawaki a wannan shafi.
Tun bayan da ya fara wannan shafin, ya fuskanci matsaloli kafin mawaka ma su aminta da shi, kafin su bada wakarsu a saka musu a shafin sadarwar. Sannan a yanzu da suka samu karbuwa kuma, mawaka na kyashin bada kudin da ka sakawa kafin a yada wakokinsu a shafukan.
Watakila sakamakon rashin sanin muhimmancin yin hakan ne yasa, yanzu ya ce akwai ma’aikata guda shida da suke aiki a karkashen Hausa Top, kuma suna tare da burin farfado da al’adun Arewa da kuma karawa da wasu shafuka irin wannan.
Facebook Forum