NIGERIA - Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya jaddada burin gwamnatin kasar na gani ta shawo kan matsalar rashin tsaro da ya gallabi sassan kasar, da suka hada da na ‘yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, da na satar mutane, da kuma fashi da makami.
Goodluck Jonathan yayi wannan ikirari ne jiya Asabar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauci, a taron gangamin da jam’iyyarsa ta PDP ta shiryawa shiyyar arewa maso gabas, da aka yi wa lakabi da sunan “Gangamin hadin kai na PDP” domin dinke barakar dake jam’iyyar.
NIGERIA - Yayin da ake cigaba da samun rabuwar kawuna tsakanin wakilai masu hallartar taron kasa, inda wasu daga arewacin kasar suka fara barazanar kauracewa taron, yanzu haka wasu gwamnoni da ma kungiyoyi sun fara mayar da martani game da dambarwar dake wakana a zauren taron.
Sai dai kalaman daya daga cikin wakilan taron, Lamidon Adamawa, yace ko yau Najeriya ta rabe, jihar Adamawa ka iya komawa karkashin Kamaru.