Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji a Najeriya Sun Kama 'Yan Boko Haram da Makamai na Harbo Jirgin Sama


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Hotunan da kungiyar ta nuna kamin akai harin da kuma bayan an kai harin akan Baga da kuma Doron baga, ya nuna gine gine 3,700 da aka kona su kurmus bada jumawa ba, bayan da kungiyar ta kama Baga ranar 3 ga watan nan na Janairu.
Galibin gidajen da mayakan suka lalata a Doron Baga ne, inda wani mai nazari na kungiyar ta Amnesty Daniel Eyre yace, "kusan an share garin baki daya, daga doron kasa, cikin kwanaki hudu kacal".
Kungiyar kare hakkin Bil'Adaman tace, a hirarraki da tayi da shaidun gani da ido, sun ce mayakan sakan sun harbe daruruwan fararen hula ciki har da yara kanana da kuma wata mace da take nakuda.
Rundunar sojojin Najeriya tace mutane dari da hamsin ne aka kashe a Baga, amma jami'ai yankin suka sai tayu wadanda aka kashen ya haura dubu daya.
Kungiyar Amnesty ta fadajiya laraba cewa, bisa laka'ari da bincike da ta gudanar ya nuna cewa Boko Haram ta kai hari kan Baga ne domin garin ya kasance sansanin 'yan kato da gora, ko civilian JTF, wadanda suke taimakawa sojoji sun yake 'yan binidgar.
Tunda farko a wunin jiya, rundunar sojojin Najeriya a shafinta a dandalin Twitter, tace ta wargaza wani yunkurin kai hari kan garin Biu da 'yan bindigar suka so suyi. Rundunar tace sojoji suna farautar 'yan binidgar bayan da suka kama biyar daga cikinsu, da makamai na harbo jiragen sama biyu.

XS
SM
MD
LG