Ga dukkan alamu dakarun Nijeriya na samun galaba kan ‘yan Boko Haram a jihar Adamawa, inda su ka kwato kusan dukkannin kananan hukumomin jihar daga hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram. Hasalima, hukumomin kai daukin gaggawa sun fara zuwa wuraren da aka kwato daga hannun Boko Haram din don ba da irin taimakon da ake bukata cikin gaggawa.
Wakilinmu a jihar ta Adamawa, wanda ya aiko ma na da wannan rahoton, Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito babban Sakataren Hukumar Kai Agajin gaggawa ta SEMA da ke jihar Alhaji Haruna Amagoro na cewa daga cikin kananan hukumomi 7 da aka sake kwatowa guda 6 na hannun gwamnatin jihar sosai. Ya ce hukumarsa ta kai kayan magunguna da abinci da sauran abubuwan bukata a kananan hukumomin. Hasalim, inji shi, jami’ansu sun kwana a irin wadannan wuraren ciki har da Michika da Wuba.
To saidai duk da wannan hobbasar, wasu masu tsokaci kan al’amuran tsaro da kuma harkokin yau da kullum na ganin akwai lauje cikin nadi dangane da abubuwan da ke faruwa. Dr. Bawa Abdullahi ya ce akwai alamomin wasu na niyyar yin kafar ungulu ga zaben Nijeriya da ke tafe saboda su dauwama bisa gadon mulki. Ya ce ana son a fake da guzuma a harbi karsana ta wajen ruruta tashin hankalin da ke faruwa don zaben ya sami matsala.