WASHINGTON, DC —
Shugabar wata kungiyar mata a Kano Hajiya Hafsat, tace tayi na’am, da dage zabe da hukumar zabe mai zaman kanta tayi a Najeriya.
Tayi wannan furuci ne a wata hira da wakiliya muryar Amurka, Baraka Bashir, a birnin Kano.
Tace dage zaben ya baiwa kungiyarsu damar cigaba da wayarwa da mata kan dangane da mahimmancin yin rajista da kuma jefa kuri’a, tace lokaci yayi da mata zasu tashi tsaye domin zaben mutane nagari .
Ta kara da cewa a wannan karon mata, ba zasu yarda, a barsu a baya ba, kuma zasu tabbatar da cewa sun kasa sun tsare sun kuma raka alkaluman zabe.