Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta dauki Hayar Mutane Su Kashe Mijinta


Wata kotu mai zama a Legas, ta bada balin wata mata mai aiki a banki mai suna Oluchi Tochukwu, akan kudi Naira miliyan daya, wanda ake zargi da niyyar kashe mijinta.

Ita dai matar an cafke ta ne bayan da aka damke mutanen da ta baiwa aikin kasha mijinta masu suna KingsleyIkechukwu, mai shekaru talatin da shida da Chigixie Smart mai shekaru talatin da biyu.

‘Yan Sandan jihar, Ogun, ne suka cafka mutanen a Ijebu Ode, akan hanyarsu ta arcewa zuwa Onitsha, a cikin motar mijinta kirar Range Rover.

Koda yake ta musanta zargin, amma mai gabatar da kara Sufeton, ‘yan Sanda, Julius Babatope,ya fadawa kotu cewa wace ake zargin ta dauki hayar mutanen su kashe mijinta a ranar 9, ga watan Oktoba, na wannan shekarar da muke ciki.

Ya kara da cewa ta ajiye masu adduna da guba da zasu yi amfani dasu wajan aiwatar da nufinsu, ita kuma ta kwashe naurar kwamfutarsa safurin HP da iPhone da takardun motarsa da aka kiyasta kudinsu Naira milyan tara da dubu daru ukku.

Da yake zartar da hukunci mai shara’a Olajuwon, ya dage shara’ar zuwa ranar 23, ga watan Janairu, da bada umarnin a ci gaba da tsare muanen biyu, ita kuwa aka bada belinta akan kudi Naira miliyan daya.

XS
SM
MD
LG