WASHINGTON, DC —
Wata mata mai suna Sarah Ademola, ta gudu ta bar ‘ya’yanta jarirai tagwaye a wani asibiti, a Legas, bayan haihuwarsu.
Ita dai wanna mata ta haifi tagwayen ne a wani asibiti mai suna Felken, a unguwar Somolu, a birnin Legas, ta bar tagwayen ne bayan da mijinta Adeyemi Ademola, ya kasa biyan kudin asibitin Naira dubu dari da hamsin (150,000).
Wata ma’aikaciyar asibitin da bata son a ambaci sunanta ta bayyana cewa tagwayen na cikin koshin lafiya, koda yake tace hukumar asibitin ta bada zuwa karshen mako su zo su karbi tagwayen ko kuma a mika su ga gwamnatin jihar Legas.