Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Yarinya Ta Kirkiro Yadda Za'a Mayar Da Leda Man Fetur


A kasar Masar, wata yariya matashiya ta kirkiro wata hanya da za’a iya sarrafa ledojin da ake zubar wa zuwa man fetur wanda darajar sa zata iya zamowa ta miliyoyin daloli a cikin shekara guda.

Matashiyar mai suna Azza Faiad ta janyo hankalin ma’aikatar binciken albarkatun man Fetur ta kasar Masar, wanda hakan ya sa suka bata damar yin amfani da dakin binciken su domin mayar da ledojin da ake zubarwa zuwa man Fetur.

Faiad ta gano hanya mafi sauki, kuma wadda za’a iya mayar da sinadarin aluminisilicate wanda nan take zai rage tsadar mayar da ledojin da aka zubar zuwa sinadarin gas mai kamar sinadarin Methane da kuma propane, wanda za’a iya mayar da shi sinadarin ethanol, abin da masu binciken kimiyya suke kira “Biofuel” a sakamakon wani sinadarin da ke cikin ita ledar ya kasance iri daya ne da wanda ake samowa a kasa domin hada wannan sinadari na ethanol biofuel.

Hakan ya kara bayyana wata hanyar da za’a iya samun wasu sauran sinadaran da za’a iya narke su domin anfani da su ta wata hanyar.

Kasar Masar dai na zubar da tarin bolar ledoji a kowace shekara, kuma binciken na Faiad ya nuna yadda za’a mayar da wannan tarin sharer zuwa adadin kudin da yawan su yakai dalar Amurka Miliyan 78 a kowace shekara.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG