Matakin da matasa musulmi suka dauka a garin Pandogari na jihar Niger kan wani dan kabilar Igbo, da makamancin sa a jahar Kano da yayi sanadiyyar hallaka wata mata na daga cikin misalan baya bayannan na daukar doka a hannu da matasan suka yi akan wadanda ba musulmi ba a sanadiyyar cewar sun yi batanci ga annabi Muhammad (SAW).
Sai dai a iya cewa gabanin wannan dabi’a ta kunno kai a arewacin Najeriya, an shafe shekaru da dama da matasa ke cinnawa jama’a wuta su kone kurmus a jihar Legas muasamman wanda aka kwarmata cewa ya saci wani abu koda kuwa da wasa ne ko kuma bisa kuskure.
Barrister Kamil Hassan Kwakwatawa wani lauya ne a jihar Kano dake nazari akan al’amurran da suka shafi yau da kullum musamman akan batutuwan da suka shafi matasa, ya ce akwai dalilan dake sabbaba irin wannan tunani a kwakwalwar matasan.
Ya ce “rashin aikin yi ko kuma wani bangare na talauci da yake addabar al’uma shine asalin abin da yake ruruta wutar rikici ko kuma daukar doka a hannu, domin kuwa a misali kamar yadda muke kallo a kwai lokutan da ake cikin talauci da yunwa da fatara, anyi ta fama da irin wadannan matsaloli sosai.”
Ya kara da cewa “daukar doka a hannu nada alaka da wahala, tsiya,yunwa da sauran su, domin kuwa idan ana cikin wadata babu yadda za’a yi matasa su kama aikata irin wadannan munanan ayyuka.
Kamar yadda lamarin ya faru a Kano, mai shagon bai yi komi ba wasu ne suka zo daga baya kawai-kawai suka dauki doka a hannun su akan wannan mata, saboda haka idan rayuwar jama’a ta inganta babu wanda zai yarda ya sa kansa cikin irin wannan mugun aiki.”
Saurari cikakken rahoton a nan.