Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talauci Na Haddasa Tsattsauran Ra'ayi


Wata kungiyar farar hula a birnin Niamey na Janhuriyar Nijar ta gudanar da wani zagaye don fadakar da matasa akan illolin daukar tsattsauran ra’ayi da kuma muhimmancin zaman lafiya a cikin kasa. Wannan zagayen ya biyo bayan kwanaki hudu da kungiyar, wadda ke kula da wanzar da zaman lafiya ta kwashe ta na fadakar da matasa a birnin na Niamey.

Gangamin ya tattara ‘yan jarida daga kafofin yada labarai dabam-dabam, da su ka yi amfani da muhimman titunan birnin Niamey suna isar da sakon ga matasa.

Malam Musa Innakaka, yana daya daga cikin ‘yan jaridar da suka halarci wannan taron. Ya fadi cewa yaki da tsattauran ra’ayi ba yaki ne na bangare guda ba, amma na kowa da kowa ne. Don haka akwai bukatar ‘yan jarida su tsunduma cikin wannan aikin don fadakar da matasa rashin ribar wannan akidar, amma akwai hanyoyin da za u taka rawa wajen ciyar da kasarsu gaba su kuma moreta.

Mallam Musa ya kara da cewa talauci na daya daga cikin abubuwan dake jefa matasa cikin irin wannan tunanin.

Amfani da matasa wajen tayar da kayar baya ya kasance ruwan dare a nahiyar Afrika. Lauya Lurwan Abdulrahaman, mai fafutika kuma a kungiyoyin farar hula a Nijar, ya danganata wannan al’amarin da jahilci da kuma zaman kashe wando da matasan Afrika ke fama da su. Ya ce ilimi na da muhimmanci sosai don yana toshe duk wata muguwar Magana ko tunani.

Ga Yousouf Abdullahi da rahoton

XS
SM
MD
LG