A yayin da kura ta lafa akan zargi da wulakancin da kulab din Arsenal ya fuskanta daga dukkan bangarori da kuma bakaken maganganun da Koch Arsene Wenger yayi bayan tashin wasan jiya laraba da aka tashi a 3 – 1, cewar wannan tamkar kashe kai ne wato barin zuciya ta jagoranci kwakwalwa.
“Kaifin tunanin mu bai kai kimar shigar mu wannan gasar ba mun dai yi kundunbala ne kawai” ya kara da cewar “mu muka jawo duk abin da ya faru damu”
Koch Wenger dai na yawaita ambaton kaifin tunani da basira koda kulab din na cikin nasara ko shan kashi.
Koda shike a wasu shekaru da suka gabata da kuma shekara ta dubu biyu da goma an kai ‘yan wasan kulab din gabadayansu wajan gwajin lafiyar kwakwalwa da ingancinta kamar yadda ake bukatar duk masu wasan motsa jiki su kasance, kuma sakamakon ya nuna cewar dukansu sun kasance masu fice kwarai.