Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tantance Wadanda Suka yi Karatun Boko


Matasa i
Matasa i

Hukumar kidayar jama'a a Najeriya, ta fara wani aikin tantance wadanda suka yi karatun boko koda na firamari ne a kasar hukumar dai tace zata dauki watani uku tana gudanar da aikin a duk fadin Najeriya.

A shekara ta 2013, hukumar kidayar jama'ar tayi irin wannan aikin amma akan fani kiwon lafiya.

Kwamishinar hukumar kidayar jama'ar mai kula da jihar Neja Barrister Aliyu Datti da yake karin haske akan wannan aikin yace makasudin wannanan shine domin sanin matsayin ilimi a kasar da sanin dalilan da suka sa yaran da ya kamata ace suna makaranta basu zuwa.

Shima shugaban karamar hukumar Rafi Muhammad Isa, yace kudirin da hukumar kidaya ta dauka na batun tantance batun ilimi yana da tasiri saboda ganin halin da ilimi ya shiga a kasar.

XS
SM
MD
LG