Yau ne a birnin Makka na kasar Saudi-Arabia ake kammala taron yini uku na shugabanni da malaman musulinci kan batun ayyukan ta’addanci da sunan addinin musulinci, wadda hakan ke bata addinin a idon duniya.
A jawabin bude taron a ranar Lahadi, daya daga cikin shehunnan malaman dake koyarwa a jami’ar Al-azar dake birnin Al-khira na kasar Masar, sheik Ahmad Al-Tayeb ya bukaci a gudanar da garanbawul a tsarin manhajar koyar da musulunci, a jami’o’i da sauran makarantun nazarin addinin musulunci a matsayin matakin magance gurguwar fahimta da wasu musulmi keyiwa Alkur’ani da koyarwar annabi Muhammadu (SAW).
Wasu malamai a Kano sun bayyana ra’ayinsu dangane da shawarar da guda daga cikin malaman da suka halarci taron ya kawo kan gudanar da manhajar koyarwa a makarantu da Jami’o’in koyar da addinnin Islama.
Amma dakta Bashir Aliyu Umar, babban limamin masallacin juma’a na Al-Furqan a birnin Kano, kuma mataimakin shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ta Afirka, mai kula da shiyyar Afirka ta yamma, yace manhajar da ake amfani da ita bata da wani matsala, galibin kungiyoyin tsaurin addini a duniya ‘yan Boko ne ke jagorantar su, kuma ma suke kafasu a wasu lokuta.
Wannan magana ce ta malamai masu koyarda addini su zama masu sassaucin ra’ayi, sune ya kamata su sami cikakkiyar dama ta fahimtar da mutane fiye da masu tsatstsauran ra’ayi.