Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Shugabannin Kamfanonin Fasaha


Hanyoyin sadarwar zamani sun zama wani babban bangare na rayuwar mutane, amma ra’ayi ya banbanta kan yadda take tasiri wajen sada zumunci ga mutane. A wajen wani taro da aka yi kwanan nan na mako gudana karawa juna sani a birnin New York.

Shugabannin kamfanonin fasaha sun nuna sabbin kayayyakin su, wadanda yawancin su ba kayan fasaha bane, amma an tsara su bisa la’akari yadda mutane zasu tuntubi junan su.

Mataimakain shugaban kamfanin Jewlbots, Scott Davison, ya bayyana yadda za a shawo kan yan mata cikin sauki, ta hanyar sarrafa abubuwan da suke so kamar kayayyakin ado domin su nuna sha’awa.

Jewelbots wani awarwaro ne da aka sawa fasaha, da misali zai yi haske dake nuni da cewa abokan hulda sun shirya ko kuma sun karato ko kuma an samu sabbin abokanai inda suka shiga wannan shafi, ko kuma ya sanar da mutum idan ya samu wani sako daga shafin sada zumunci.

XS
SM
MD
LG