Akwai bukatar a taimakama mata a kowane irin bangare, mussamman ma ta bangaren ilimi don suyi dai daito da zamani. Shugaban wata kungiyar mata a jihar Jigawa, Ita dai wanna kungiyar me suna Gangirin Yamma, kungiyace wadda take taimakama mata wajen iya dogaro da kai, shugaban kungiyar Malam Muhammad Akibu, yayi bayanin irin aikin da kungiyar tasu takeyi, wajen kokarin ilmantar da mata yadda zasu iya yin lissafi, ganin sun shiga harkar kasuwanci, to akwai bukatar a ilmatar dasu ta yadda zasu iya yin lissafi su iya banbance uwar kudi da riba.
Su dai a wannan kungiyar suna sarrafa gyada, inda suke cire mai da tunkuza su kuma sayar, kuma suna wannan aikin ne ta hanyar zamani nayau da kullu. Babban kalubalansu shine na yadda wadannan matan basu da ilimi na zamani, amma suna iya kokari su ga cewar an wayar musu da kai kuma ansama musu abubuwan da suka dace. Yayi kira ga al’uma dasu yi kokari su dinga siyan man da suke samarwa don tallafawa mata dama kungiyar baki daya.