Kamfanin kera wayar hannun zamani mafi girma a China Xiaomi, zai fara sayar da abin sauraran sauti wato head phone da agogon hannu na zamani da sauran lataroni masu nasaba dasu a nan Amurka ta yanar gizo cikin ‘yan watanni masu zuwa, wanda wannan tamkar kutse ne ga shiyyar kamfanin Apple, duk da kamfanin na Xiaomi bazai saida na’urar Mi 4 da akafi sanin shi da ita ba.
Bayan manyan kamfanonin fasaha na Samsung da Apple, yanzu haka Xiaomi shine kamfanin kera wayoyin hannu na uku a duniya. A jerin sabbin zuba hannun jari ya sa darajar kamfanin Xiaomi yakai dala biliyan arba’in da biyar, hakan na nufin kamfanin Xiaomi shine kamfanin fasaha mai zaman kansa mafi daraja a duniya.
Kamfanin ya fitar da kan wayar sa ta Mi 4 wadda ta zamanto ita ce wayar farko shekaru biyar da suka wuce , kuma tayi tasiri a ciki da wajen kasar China.
A yanzu haka kamfanin ya zama fitacce a duniya, wanda ke kera kayayyakin fasaha na wayar zamani da ake sayar da su akan yanar gizo kawai, a watan Fabarairu ne dai Xiaomi ya fitar da sanarwar zai bunkasa kasuwar sa zuwa kasashen yankin latin na Amurka.