Jami’ai sunce sun kama wata mata ‘yar asalin Canada, wadda ke kokarin shigar da tabar wiwi mai yawan gaske ta hanyar boyeta jikin wani teburi da ake wasan foosball.
Jami’an dake tsaron iyakar Amurka da Canada ne suka bayyana cewa an tsayar da matar ne alokacin da take kokarin tsallaka iyaka.
Inda tace musu ta na kan hanyarta ne zuwa jihar New York, domin sayen tikitin cacar nan ta Powerball mai ‘dan karen kudi, amma lokacin da ma’aikatan suka binciki motar da take tukawa, sunyi kicibus da tabar wiwi ‘daure cikin ledoji an sakaye ta jikin teburin foosball.
Jami’an dai sunce sun kama tabar wiwi da takai kudi dalar Amurka $60,000. An mika matar ga jami’an ‘yan sanda na Jihar New York.
Ranar da wannan abu ya faru aka kame wani mutum da ke kokarin tsallakawa iyakar Amurka ‘dauke da wasu haramtattun magunguna da dole sai likita ya rubawata mutum, kafin mutum ya samesu.