WASHINGTON, D C —
An umarci matasan Najeriya dasu tashi tsaye domin yakar cin hanci da rashawa a matsayin su na shuwagabanin gobe.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ne ya yi wannan kiran a lokacin da ya jagoranci wani gangami game da cin hanci da rashawa wanda kungiyar matasan Najeriya, suka shirya.
Ya ce 'yan siyasa sun dade suna amfani da matasa wajan almundahana masamman a faggen siyasa, yana mai cewa tilas ne yanzu irin wannan dabi'ar ta sake zani.
Mataimakin Gwamnan jahar Katsina, Manir yakubu ya fufawa Sanata Ibrahim Mantu baya wajan sa hannu akan rajistan yaki da cin hanci da rashawa.