Barazanar matukar ba Goodluck Jonathan, bane ya lashe zabe za’ayi uwar watsi a Najeriya, ba zai jawo yak,i ko tada wata fitina ba, in ji shugaba Goodluck Jonathan, a taron zantawa da manema labaru, zantawan daya ta’allaka kan babban zaben Najeriya.
Shugaba Jonathan, yace da yawacin shirye-shirye, da akeyi ko tallace-tallace, kan kamfe dinsa dake kunshe da kausasan kalamai, ko kage bai san masu yi ba da kusan kashi, tamanin cikin dari ba.
Shugaban dai ya musanta tura shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega, hutun dole gabanin kamala wa’adinsa, a watar Yuni, da hakan zai bashi damar nada sabon shugaba da zai zama dan amshin shata.
Irin wannan barazanar ta guguwar shirya zaben har ta sa jama’a. kauracewa inda suke zuwa tudun muntsira.
Tsohon shugaban mulkin soja, janar Abdulsalam Abubakar, yace toh yanzu yakamata, a kwantar da hankali, da fatar gudanar zaben cikin lumana ne mafi a’ala.
Janar Abdulsalam, yace “ Wadanda suke tada hankali, akan wasu mutane, wa’anda akeyi dominsu basu san anayi ba, sun kwance a gidajensu, talaka yana nan yana shan wuya, kuma talakawan Najeriya, ne ke wannan aika-aika, sabili da haka kowa yawa kansa qiyamul Laili, ya san tada hankal;I baida amfani, ina kuma fata su masu zaben zasuyi gaskiya.”
Rahotani dai na nuni da cewa shugaban hukumar zabe, na cigaba da shirin gudanar da zaben, zuwa ranar 28 ga watan gobe.