Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadda Kotu Ta Daure Kan Kin Bada Lasin Auren Jinsi Ta Koma Aiki


Wata akawun kotu da ta bijirewa umurnin kotu, da aka rufe a gidan wakafi don kin bada lasi ga masu auren jinsi daya, ta koma bakin aiki yau litinin, tana mai cewa ba zata hana abokan aikinta bada lasisin ba amma kuma ta ce menene fa’idar takardar ba tare da sa hannunta ba?

Kim Davis ta je kotun garin Rowan dake jihar Kentucky bayan da aka garkame ta har na tsawon kwanaki 5. Alkalin wata babar kotu ya rufe ta bayan da ta ki bin umurnin sa a kan batun bada lasi, bisa ga doka kotun kolin Amurka da aka fidda a watan Yuni mai cewa masu auren jinsi na da ikon yin aure bisa ga dokar kasa.

Ms. Davis dai krista ce ‘yar darker Apostolic, tace auren jinsi ya saba wa addininta. Ta zama jaruma ga wasu kiritoci masu ra’ayin rikau a nan Amurka akan kin bada lasisi ga masu auren jinsi.

Yayinda aka bude ofishinta, Ms. Davis ta karanta wata takarda da aka rubuta da hannu, tana mai cewa “ba na son wannan cece-kuce. Bana kuma so a sani gaba, kuma bana so a raina ni”.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG