Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ba-Indiye Mai Mata 39, Ya Ce a Shirye Ya Ke Ya Kara Aure


Wani Ba-indiye dan shekaru 66 da haihuwa na da mata 39, 'yaya 94 da jikoki 33 kuma duk a gida daya suke zama.

Wannan iyali dai suna zama ne a wani bene mai hawa 4, mai dakuna 100 a wani kauye da ke jihar Mizoram, kusa da iyakar kasashen Burma da Bangladesh.

Ziona Chana ya ce " na taba auren mata 10 cikin shekara guda".

Matan Ziona na zama a wani babban daki kusa da turakarsa, kuma 'yan garin sun ce yawancin lokaci yana kasancewa da mata 7 zuwa 8 a gefensa, a koda yaushe.

'Yayan Ziona maza da matansu, tare da duk jikokinsa kowa dakinsa da bam amma wurin dafa abinci daya suke amfani da shi.

atan Ziona sukan raba girkia tsakaninsu, 'yayansa mata kuma ke yin sauran ayyukan gida kamar shara da wanke-wanke, su kuma mazan su ke kula da harkokin waje kamar kiwon dabbobi, noma da sauran abubuwa.

wannan iyali dai su 167 ne dukansu, kuma sukan ci kusan buhun shinkafa daya da na dankali daya a rana.

Ziona ya ce "a shirye na ke in kara fadada iyalina haka kuma a shirye na ke in sake aure.

XS
SM
MD
LG