WASHINGTON, DC —
Wani mutumin da aka sace masa diya a cikin daliban makarantar mata ta Chibok a Jihar Borno, ya bayyana cewa har yanzu sun kasa samun kwanciyar hankali a saboda wannan ukuba da 'yan Boko Haram suka jefa su ciki.
Yace sun kai kwanaki biyar shi da maidakinsa ba su iya cin abinci, ba su iya barci, a saboda bakin ciki da fargaba na wannan abu da ya faru. Yace har yanzu kamar zaman jimamin mutuwa ake yi a gidansu.
Yace jami'an tsaron da suka fara arangama da 'yan Boko Haram a ranar da abin ya faru, sun yi kokari, amma an fi su yawa an kuma fi su makamai ne. Yace daga baya, wasu sojojin sun zo daga Maiduguri suka bi sawun 'yan bindigar, amma su ma sun tarar an fi karfinsu suka janye.
Ga dai bayanin da yayi nan...