Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Yayi Tattaki Har Birnin Washington da Niyyar Satar karen Gidan Shugaba Obama


An kama Wani mutum dan asalin jihar North Dakota, a Amurka da yayi niyyar satar daya daga cikin karnukan gidan shugaba Obama, dauke da bindigogi da albarusai a wani gidan saukar baki da ke birnin Washington DC.

Bayanin shirin satar daya da ga cikin karnukan na gidan shugaba Obama, masu suna Bo da Sunny da mutumin mai suna Scott D. Stockert, dan shekaru 49 da haihuwa da ga birnin Dickson na jihar North Dakota yayi, ya je ga kunnen Ofishin hukumar leken asirin Amurka da ke Minnesota.

A lokacin da Stockert ya tuko akori-kurarsa (mota) daga North Dakota zuwa birnin wasihngton, ba tare da bata lokaci ba jami’an leken asiri su ka gano inda ya sauka a kusa da fadar White House. Jami’an sun sami Scott dauke da bindigogi iri biyu a motarsa, da albarusai da adda, kuma takardun kotu sun nuna cewa Scott ba ya da izinin mallakar makami, sai suka kamashi.

Jami’an hukumar leken asiri sun shaida a wata takardar kotu cewa, a lokacin da aka kama Scott, yayi wa jami’an maganganun da ba su da kan gado, ciki harda cewa shi dandan tsohon shugaban kasar Amurka ne, marigayi John F. Kennedy da wata tsohuwar tauraruwa mai suna Marilyn Monroe. bayan haka ya gaya masu cewa ya na shirin tsayawa takarar shugaban kasa.

Scott dai ya yarda cewa ya je birnin Washington ne da niyyar satar Bo ko Sunny. Yanzu haka dai ana tuhumarsa da laifin daukar bindiga a wajen gidansa ko wajen sana’arsa, abin da kuma doka ta haramta a yankin gundumar Columbia.

A wani zaman farko da aka yi jiya Jumma’a, an saki Scott amma an sa shi a wani shiri na sa ido kafin ranar da za a je kotu akan laifin da ake tuhumarsa da shi. An kuma haramta mashi daukar kowanne irin makami ko kuma zuwa kusa da fadar white House.

XS
SM
MD
LG