Tun bayan bullowar kafofin sada zumuncin zamani kamar su Facebook da Twitter da makamantan su, wasu al’ummomi ke danganta su da kafofin yada rigingimu da tada husuma, bisa la’akari da ‘yancin da jama’a ke da shi na aikawa da sakonni ba tare da shamaki ba, sakonnin da wasu ke gani sun taimaka wajen azazzala rikicin addini a Najeriya.
A kasashen da suka cigaba, inda kuma ake aiki da doka da oda, bisa mutunta ‘yancin bil’adama amfani da kafofin yada labarai, wata dama ce ta bayyana ra’ayi domin amfanin jama’a da kuma kasa baki daya.
To sai dai a kasashen da suka yi kaurin suna wajen kama karya da rufa-rufa a harkokin gwamnati, amfani da wadannan kafofin zamanin tamkar shiga sharo ba shanu ne da kuma barazana ga harkokin tsaron kasa. Batun da ke neman kunno kai yanzu haka a wasu sassan Najeriya, inda aka fara zargin wasu masu amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen haddasa husuma da ya kan kai ga daukar fansa, lamarin da ya sa wasu sake tunanin akan amfani da shafukan sadarwar na zamanin.
Barista Danlami Wushishi yana daya daga ciki masu amfani da hanyoyin sadarwar na zamani, ya fadi cewa yana dari-dari da yin amfani da kafofin na zamani. Ya kuma ce abin takaice ne yadda wasu musamman matasa ke yada labaran da ba na gaskiya ba.
Yayinda wasu ke gani akwai bukatar daukar matakai na taka-tsan-tsan, da kuma sa ido akan harkokin masu amfani da wadannan kafofin, wasu masu fafutukar kare hakkin bil’adama na gani shiga hakkin fadin albarkacin bakin jama’a ne idan aka dauki wani mataki na takaita yin amfani da shafukan.
Komared Abubakar Idris, na kungiyar kare hakkin bil’adama ta Peoples Rights Advocacy for Social Justice ya fadi cewa rigingimun da ke faruwa a Najeriya sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari don ba kowa ke da na’urorin amfani da shafukan ba. Ya kuma kara da cewa muddin Shugabannan kasa za su cigaba da ciyar da al’ummarsu da guba akan fadin abinda basu aikata ba, to dole hakan ya haddasa jita-jita.
Kamar yadda za ku ji anan ga Babangida Jibrin dauke da rahoton.