Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwa Ta Kunno Kai a Jihar Taraba


Para jamaah Haji mengunjungi gua Hira, di puncak Jabal Al-Noor, Mekkah, tempat di mana Nabi Muhammad SAW menerima wahyu untuk pertama kalinya.
Para jamaah Haji mengunjungi gua Hira, di puncak Jabal Al-Noor, Mekkah, tempat di mana Nabi Muhammad SAW menerima wahyu untuk pertama kalinya.

Yanzu haka,wata sabuwa ta kunno kai a faggen siyasar jihar Taraba, inda ake kaiwa yan takara hari yayin gangamin kamfe, batun dake kara tada hankulan jama'a, a fadi jihar ta Taraba.

Cikin wadanda suka hadu da fushin magoya bayan 'yan siyasa har da tawagar mukaddashin gwamnan jihar dana 'yan takarar PDP,da SDP.

Yanzu haka an soma musayan kalamai a tsakanin jam’iyyun siyasa, a jihar Taraba, game da hari-haren da ake kaiwa ‘yan takara yayin gangamin kamfe wanda a wasu lokuta kan jawon hasarar rayuka.

Duk jam’iyyun jihar na zargin juna dagane da hare-haren dake faruwa a wuraren kamfe.

Gwamnan jihar Sani Danladi, daya ke jawabi kan hare-haren yace an ci masa mutunci, amma yayi hakuri, ya yafewa kowa, yace amma duk wanda yace ba zaiyi biyayya ga Gwamnati ba toh zai gamu da hukuma.

Dambarwar Siyasar Taraba - 3"28"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG