WASHINGTON DC, —
'Yar wasan kwallon kafa ajin mata daga Najeriya Uchenna Kanu, ta lashe kyautar gwarzuwa 'yar wasan kwallon mata ta kasar Amurka, kungiyar da take shirya wasanni motsa jiki ta kwallejin (Association of Intercollegiate Athletics) ce ta bada wannan lambar yabon.
Mujallar Goal.com, ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewar an karrama 'yar wasan Kanu da wannan kyautar gwarzuwa, sakamakon kwazon da tayi a wannan shekarar a Amurka.
Jami'an hukumar kula da kwallon kafa ta Mata (NAIA) su goma sha daya ne suka yi zaben bada wannan kyautar a ranar Laraba da ta gabata. Uchenna Kanu, tana buga wasan tane a kwalejin Amurka wato (American College), dake kudu maso kudu.
Facebook Forum