Wata yarinya mai suna Esther Okade, ‘yarshekaru 10 da haiwuwa, da ke zaune a Ingila tare da iyayenta amma ‘yar asalin kasar Nigeria, ta sami shiga wata jami’a a can Ingila don karanta lissafi. Inji kamfanin jaridar Bella Naija.
Babban bambancin dake tsakanin Esther da sauran yara shine yadda duk da karanchin shekarunta ta sami shiga jami’a don samun digiri a fannin lissafi duk da cewa bata je makaranta ba.
Abun tambaya anan shine, yaya za ace yaro bai je makaranta ba amma ya sami shiga jami’a? A abin mamaki shine ita dai Esther da kaninta Isiah dan shekaru 6 da haihuwa, mahaifiyarsu mrs Omonefe ce ke koyar da su a gida.
Kamfanin na Bella Naija ya kuma fadi cewa, Mahaifiyar yaran ‘yar shekaru 37, wadda ke da digiri a fannin lissafi, ta fadi cewa diyarta na bada himma sosai don ko a kwanan nan ma ta rubuta wata jarabawa a makarantar kuma ta sami dari bisa dari.
Ita dai Esther ta rubuta jarabwar shiga jami’a ko kwaliji da ake kira GCSE a takaice a lokacin da take da shekaru shidda da haihuwa. Haka kuma kaninta Isiah, shima yana nan yana shirin rubuta jarabawar ta shiga jami’a.
##caption:Ilimi.##