Rundunar ‘yan Sandan jihar Ogun, ta cafke wani matashi Segun Ogunlusi, mai shekaru 33, wanda ake zargi da kisan mahaifiyar sa Abimbola Ogunlusi, mai shekaru 60.
Wannan mummunar lamari ya faru ne ranar talata, a gida mai lambar 16, layin Oketunde, a unguwar Molatori, a karamar hukumar Ogijo Sagamu, dake jihar Ogun.
Rundunar ta cafke shine bayan da ta samu rahoton wannan aika aika daga bakin kanwarsa mai suna Yetunde Ogunlusi.
A cewar Yetunde, ta bar mahaifiyarta a gida kafin ta wuce zuwa wajan aiki da safe koda ta dawo gida baya kafe bakwai na dare bata tarar da mahaifiyar nata ba sai ta tambayi shi yayanta amma bai bata amsan da ta gamsu ba sai ta kai rahoto ga hukumar ‘yan Sanda.
Da take tabbatar da lamarin kakakin ‘yan Sandan, jihar ta Ogun,Abimbola Oyeyemi, tace ana bin diddigin dalilin da ya jawo wannan tu’annati.