WASHINGTON, DC —
Inna da rawar takawa ne ya sa mai horas da ‘yan wasa na Super Eagles, Sunday Oliseh, ya bukaci in zo in murza wa kasata leda, in ji Emmanuel Emenike.
Dan wasan gaba wanda a yanzu haka aka bada aron sa ga kungiyar Qatari, ya kasance dan wasan Najeriya da yafi kowa jefa kwallaye a raga a gasar kasashen nahiyar Afirka, wanda aka buga a Afirka ta kudu shekaru biyu da suka gabata.
Shi dai Emenike, sun bata da tsohon mai kula da kungiyar ta Super Eagles, Stephen Keshi,wanda ya daina saka shi a wasan tun bayan wasan da ya buga wa Najeriya, a shekarar 2014, lokaci da suka kara da Sudan.
Yace kungiyar Super Eagles bana wani mutun daya bane na duk ‘yan kwallon ne duk lokaci da aka nemeni naka yiwa kasata wasa da karamci da kuma girmamawa.