Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Yanke Shawarar Dawowa Ne Saboda Muhimmancin Wasan Dake Tafe


Members of the Super Eagles, Nigeria's national team, train in Abuja October 10, 2013 before World Cup qualifier against Ethiopia.
Members of the Super Eagles, Nigeria's national team, train in Abuja October 10, 2013 before World Cup qualifier against Ethiopia.

Mai horar da ‘yan wasan Super Eagles, Sunday Oliseh, ya amsa cewa lallai bai gama murmurewa daga rashin lafiyar da ya ke fama da ita ba, lamarin da ya sa aka garzaya da shi kasar Belgium domin neman magani.

Oliseh ya bayyana cewa, ya yanke shawarar ya dawo gida ne domin fara shirin wasan fidda gwanayen da za su halarci

Gasar Cin Kofin Duniya a shekara mai zuwa, inda Najeriya za ta kara da kasar Swaziland.

Ya ce yanke shawarar dawowa ne saboda muhimmancin wasan.

A cewar mai horar da Super Eagles din, ‘yan wasansa a shirye suke, kuma ya yi amannar za su lashe dukkanin wasanninsu domin samun gurbin shiga gasar.

Ya kuma furta cewa ba za su raina ‘yan wasan na Swaziland ba, domin za su iya kawo cikas ga Najeriya a yunkurinsu na shiga gasar, ganin cewa sun mamayi ‘yan wasan Guinea a baya.

Tuni dai rahotanni suka nuna cewa dukkanin ‘yan wasan Super Eagles sun isa sansaninsu da ke Abuja, inda Obafemi Martins ya kasance dan wasa na karshe da ya isa da misalin karfe 6.30 na safiyar yau Laraba.

XS
SM
MD
LG