Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Damfara Da Sunan 'Yan Siyasa Da Jami'an Gwamnati


Rudunar ‘yan Sandan Najeriya ta damke wasu mutane hudu da suke suka kware wurin damfarar mutane masamman ‘yan kasashen waje wurin amfani da sunayen wasu fitattun manyan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati.

Su dai wadannan mutane ana zargin sune da amfani da layuka masu dauke da sunayen manyan ‘yan siyasa kamar shugaban ma’aikatar fadar suhgaban kasa Cif Bola Tinubu, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a cikin kasarsuna damfarar mutane miliyoyin Nairori.

An same su da layuka a cikin wayoyi dabam dabam goma sha biyar masu rajista da sunayen manyan jami’an gwamnati da wasu layukan a hannun wadannan mutane a lokacin da aka kamasu.

Wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata wannan laifin kuma sun samu kudade da suka kai miliyan ashirin a wannan sana’ar damfara a cikin watanni shida.

Wata majiya a hukumar ‘yan sanda ta fadawa ‘yan jarida cewar an kama wadannan mutane ne biyo bayan kara da aka shigar a kansu.

Majiyar tace bayan jerin kararraki da sufeto janar (IGP) ya samu a kan wasu gawurtattun miyagu masu amfani da sunayen manya a cikin kasar kamar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, da NSA, da ministan albarkatun mai, da ministan kundi, da Cif Bola Tinubu, da shugaban majalisar dattawan kasa, hakan ne yasa Sufeto janar Ibrahim Idris ya umarci sashen leken asiri na ‘yan Sandan da su tabbatar da ganin cewa sun gano da kuma kamo wadannan miyagu mutane masu aikata wannan aika aika a cikin Najeriya.

XS
SM
MD
LG