Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mata Kada Wani Kalubale Ya Sa Kuyi Kasa A Gwiwa -Inji Shamsiyya Faruk


A shirinmu na mata da suka taka wata muhimmiyar rawa a al'ummar su, a yau dandalin VOA ya sami zantawa da wata matashiya mai suna Shamsiyya Faruk daga jahar Kano.

Malama Shamsiyya ta ce, ta fuskanci kalubalen da kafin ta samu karanta diploma a aikin jarida sai da ta tsaya tsayin daka sa'annan ta kai labari.

Ta ce sai da ta rubuta jarabawa na Jamb sau biyu bata sami gurbin karatu ba a jam'ia da taga lokaci na neman ya kure ma ta, ta yanke shawarar karantar diploma a harkar jarida.

Ta ce duk da rashin samun gurbin karatun, hakan bai zai hana mata yin digiri ba a rayuwa. dan haka tana kira ga sauran 'yan mata da su cigaba da kokarin neman ilimi domin ciyar da al'umar su gaba. ta kara da cewa kada wani kalubale ya sa su yi kasa a gwiwa.

Saurari cikakken shirin

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG